Soke ganawar Trump da Kim Jong-un na daukar hankalin duniya
May 25, 2018A wasikar da fadar White House ta aikewa shugaba Kim, Trump ya ce shugaban Koriya ta Arewa na kuri da karfin makaman nukiliya, amma ya ce Amirka na da kayan yaki da ba a taba amfani da su ba, kuma karfin sojojinta ya zarta misali.
Da ya ke jawabin kaddamar da shirin rage amfani da manyan makamai a jami'ar Geneva, sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antoniyo Guteres, ya bayyana takaici kan maida hannun agogo baya tsakanin shugaba Trump da Kim Jong-Un.
Shi ma ana shi bangaren sahugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Ja in, ya yi kiran taron gaggawa da manyan jami‘an kwamitin tsaron kasar, inda ya bayyana rashin tasrin matakan karfi kan sasanta bangarorin biyu. Moon ya kuma jaddada fatan ganin an cimma daidaton zaman lafiya a yankin Koroyiyin biyu.
Sao'i kalilan da rusa tashohin gwajin makaman nukiliyar Koriya ta Arewa shugaba Trump, ya bayyana cewa ba zai hada ido da Kim ba kamar yadda aka shirya ganawar da za su yi a ranar 12 ga watan Yuni, ya kuma kare matakinsa da martanin fushi da Koriyar ta yi kan kalaman mataimakin shugaban Amirka Mike Pence da ya ce Koriyar za koma tamkar Libiya matukar ba ta sauya tunani kan makaman nukiliya ba.
Sai dai Koriya ta Arewar ta ce kofa a bude ta ke domin tattaunawa da Amirka a kowani lokaci.