1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da luguden wuta a wasu yankuna na kasar Sudan

Binta Aliyu Zurmi
July 16, 2023

A Sudan ana ci gaba da luguden wuta a biranen Khartoum da ma yankin yammacin Dafur a cewar shaidun gani da ido, duk da yunkurin kawo karsehn rikicin da kashen duniya ke yi.

https://p.dw.com/p/4TyPt
FILE PHOTO: Sudan's Khartoum running low on food and medicine as fighting rages
Hoto: El-Tayeb Siddig/REUTERS

Wani mumunan hari da aka kai ta sama a garin Ombada mai yar tazara da birnin Khartoum, ya yi sanadiyar rayukan mutane 5 yayin da wasu 17 suka jikkata.

Masu aikin ceto na ci gaba da neman mutane da suka makale a baraguzen gine-gine, lamarin da ya sa ake ganin adadin wadanda suka mutu ka iya karuwa.

Ya zuwa yanzu, sama da mutum dubu uku ne rikicin na Sudan mai tushe da batun shugabanci suka rasa rayukansu, a cewar wata kungiya mai tattara bayanan yaki, amma kuma wasu na ganin adadin ya zarta haka.

A jiya Asabar ne aka koma teburin tattaunawa a tsakanin sojojin gwamnati da na dakarun RSF a birnin Jeddah na kasar Saudiyya. Zaman da kawo yanzu babu rahoto a kan yadda ya kaya, a baya an yi irinsa ba tare da cimma matsayar kawo karshen yakin ba.