1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zaɓi Nkosazana Dlamini Zuma a matsayin babbar Komishiniyyar Hukumar zartaswa ta AU

July 16, 2012

Bayan lokaci mai tsawo na taƙƙaddama a karon farko Hukumar zartsawa ta ƙungiyar tarayya Afrika ta sami shugaba mace.

https://p.dw.com/p/15YQo
African leaders pose for a group photograph with U.N. Secretary-General Ban Ki-moon during the 18th African Union (AU) summit in Ethiopia's capital Addis Ababa January 29, 2012. REUTERS/Noor Khamis (ETHIOPIA - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Bayan watani uku na tankiya, a ƙarshe Kungiyar Tarayyar Afirka ta zaɓi Nkosazana Dlamini-Zuma a matsayin sabuwar shugabar hukumar zartaswa ta AU, domin maye gurbin Jean Ping da ya sha ƙasa.

An shirya wannan zaɓe a taron ƙolin shugabanin ƙasashen ƙungiyar Tarayya Afirka a birnnin Addis Ababa na ƙaysar Ethiopiya.

Taron na shugabanin ƙasashen ƙungiyar Tarayya Afirka an tsara zai tattana batutuwa daban-daban da suka haɗa da riginginmun da ake fama da su a wasu ƙasashen nahiyar hasali ma Mali, Guinea Bissau, Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo da kuma rikici tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu, to saidai maimakon hakan, batun zaɓen saban shugaban hukumar zartaswa ta fi ɗaukar hankalin mahalarta taron.

A watan Janairu na wannan shekara, shugaban Afrika su ka kasa zaɓe tsakanin Jean Ping na ƙasar Gabon wanda ke riƙe da matsayin tun shekara 20o8 da kuma Nkosazana Dlamini-Zuma ta Afirka ta Kudu.

African Union Commission chairman Jean Ping arrives for the 18th African Union (AU) Summit in the Ethiopia's capital Addis Ababa, January 29, 2012. REUTERS/Noor Khamis (ETHIOPIA - Tags: POLITICS HEADSHOT)
Jean PingHoto: Reuters

Taron na ƙungiyar Haɗin kan Afrika ya umurci shugaban AU Thomas Yayi Boni na ƙasar Benin ya ci gaba da tattanawa da 'yan takara biyu, domin warware wannan rikici ta yadda a taro na gaba, wato wanda aka kammala jiya a samu masalaha.

To saidai duk da da masanyar ra'ayi da aka yi tsawan watani da dama, an fuskanci ƙiƙi-ƙiƙa a wannan zaɓen.Sai bayan zagaye na uku 'yar takara Afrika ta Kudu ta samu nasara da ƙuri'u 37, wato kashi 60 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa.

Zaɓen ƙarara ya nuna rabuwar kanu tsakanin ƙasashen Afrika masu amfani da halshen farasanci ,wanda suka goyi bayan Jean-Ping da kuma ƙasashen da ke amfani da halshen Turanci wanda suka marawa Dlamini Zuma baya.

To saidai a jawabin da ta yi jim kaɗan kafin ana zaɓe ta Nkosazana Dlamini-Zuma ta yi kira da cewa:

"Duk ko ma wa aka zaɓa cilas ya yi aiki da kowa, wanda suka zaɓe shi da wanda ba su bashi haɗin kai, cemma shi zaɓen demokraɗiya haka ya gada, mutum ya kada ne ko kuma a kada shi".

South African Home Affairs Minister Nkosazana Dlamini-Zuma addresses the media during the leaders meeting at the African Union (AU) in Addis Ababa July 15, 2012. African leaders brought together the presidents of feuding neighbours Sudan and South Sudan on Saturday and fleshed out a plan for military intervention in northern Mali where they said al Qaeda-linked rebels threatened the continent's security. REUTERS/Tiksa Negeri (ETHIOPIA - Tags: SOCIETY POLITICS)
Nkosazana Dlamini-ZumaHoto: Reuters

Sabuwar shugabar hukumar zartsawa ta ƙungiyar taraya Afirka na da sheakru kusan 63 a duniya,ta yi karatun likita da na diplomatiya,sannan ta auri shugaban Afirka ta Kudu mai cin yanzu Jacob Zuma kamin daga bisani su rabu.Dlamini Zuma ta rike manyan muƙamai a gwamnatin Afirka ta Kudu.Ta yi zama ministar kiwan lafiya da kuma ministar harakokin wajen a gwamnatocin da suka gabata.Kafin a zaɓe ta shugabar Hukumar zartsawa ta ƙungiyar AU ta na riƙe da matsayin ministar cikin gida.

Al'umar Afrika ta Kudu sunyi mata kyakyawan yabo ta fannin jajurcewa wajen aiki, saboda haka wasu ke mata taken mace mai kamar maza, ko kuma 'yar sarki mai takalmin ƙarfe kowa ki taka ya taku.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Abdullahi Tanko Bala