Majalisar Dinkin Duniya ta fidda rahoto a kan Yemen
August 29, 2018Rahoton irinsa na farko tun bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta umarci hukumar ta gabatar da bincike a kan fyade da tirsasa yara kanana shiga aikin soja da tsare al'ummar kasar ta Yemen a gidajen yari da kuma gana wa mutane azaba da ya zama ruwan dare tun bayan barkewar rikici a kasar, ya janyo wa kasar Saudiyya matsin lamba daga kasashen duniya da kuma kungiyoyin kare hakkin dan Adam.
Tun bayan da 'yan tawayen Houthi suka hambarar da gwamnatin Yemen a shekara ta 2015 Saudiyya ta dauki alwashin ganin bayan 'yan tawayen na Houthi lamarin da ke ci gaba da janyo asarar rayukan fararen hula.
Da yake mayar da martani a kan wannan zargi jakadan kasar Saudiyya a Yemen ya ce wannan batu ne marar tushe.
Hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya dai ta bayyana gwamnatin Yemen da kasashen Daular Larabawa da kuma kasar Saudiyya a matsayin kasashen da ke aikata laifukan yaki a kasar Yemen.