An yiwa shugaban Brazil bore
September 8, 2016Daruruwan masu zanga-zanga da yawansu ya kai sama da 600 dauke da kwalayen rubutun " ba mu amince ba", " ba ma bukata" a manyan titunanan kasar Brazil suka yi wa sabon shugaban rikon kwarya na kasar Michel Temer bore a yayin da ya halarci bikin ranar 'yancin kasar a garin Brasiliya da kuma bikin bude wasannin nakasassu a birnin Rio de Janeiro a ranar Laraba.
Wadannan bukuwa biyu dai, su ne bukuwa na farko da shugaba Michel ya fara halarta tun bayan da karbi ragamar shugabancin kasar a ranar 31 ga watan Augusta bayan da 'yan majisun dattawa suka tsige Dilma Rouseff a kan zargin ta da yiwa kasafin kudin kasar kasatalanda.
Wannan dai alama ce da ke nuna irin cikas da siyasar kasar Brazil ke ci gaba da ruruwa, ko da yake daman magoya bayan tsohuwar shugaba Dilma Rouseff sun yi fargabar tsigeta zai haifar da rikita-rikitar siyasa a kasa da ka iya rikidewa zuwa yakin basasa.