Kwamitin Sulhu ya nemi a kawo karshen fadan Habasha
November 6, 2021Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya sake yin kira da babban murya kan kawo karshen rikicin kasar Habasha da ya ce ya jefa fararen hula cikin tsanani ba tare da samun damar isar musu da agaji ba. Kwamitin ya kara baiyana fargaba kan illolin da rikicin zai haifar ga tsaron kasashen da ke makwabtaka da Habashan inda ya nemi bangarorin biyu da su kawo karshen musayar munanan kalaman da ke rura wutar rikicin.
Sanarwar da kwamitin ya fitar da aka kuma gabatar ma manema labarai, na dauke da saka hannun kasashe akalla goma sha biyar mambobin kwamitin.
A dai ranar Alhamis da ta gabata aka cika shekara guda cur da barkewar rikicin da ya rikide zuwa yakin basasa. Dubbai sun rasa rayukansu wasu miliyoyi sun rikide zuwa 'yan gudun hijira a sakamakon tashin hankali a tsakanin bangaren gwamnati da mayakan kungiyar kwatar 'yancin kan yankin Tigray.