1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

An yi gargadin illar yakin Gaza kan tattalin arzikin duniya

Zainab Mohammed Abubakar
February 12, 2024

Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF da Bankin Duniya sun yi gargadin cewa yakin Gaza da kuma hare-haren da ake kaiwa kan jiragen ruwa a tekun Bahar Maliya na barazana ga tattalin arzikin duniya.

https://p.dw.com/p/4cJI5
Kristalina Georgiewa
Hoto: Ahmed Yosri/REUTERS

Yakin Isra'ila da Hamas da ya barke tun watan Oktoba tuni ya yi illa ga tattalin arzikin yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka, in ji shugabar asusun lamuni na duniya, Kristalina Georgieva.

Georgieva ta shaida wa taron gwamnatocin duniya a taron shekara-shekara na 'yan kasuwa da shugabannin siyasa a Duba cewar, hakan zai iya yin mummun tasiri na tsawoin lokaci idan har ba a dakatar da yakin akan lokaci ba.