1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi Allah wadai da harin bam a Kaduna

Usman ShehuApril 9, 2012

Ƙungiyoyi a ciki da wajen Najeriya sun tir da harin bam da aka kai Kaduna ranar bikin Easter, sai dai gwamnati ta yi gum

https://p.dw.com/p/14ZoV
epa03175758 Nigerians look on at the damage after a suicide bomber detonated a car bomb in Kaduna, Nigeria 08 April 2012. Reports indicate two car bombs exploded in Kaduna in the north of Nigeria killing at least six and injuring several people. The blasts in a built up area next to a restaurant and church caused extensive damage. Hundreds of lives have been claimed in similar terror attacks in recent months due to religeous conflict. EPA/STR pixel
Hayaki ke tashi inda aka kai harin bam a KadunaHoto: picture-alliance/dpa

A wani abun dake zaman ba saban ba gwamantin Tarrayar Najeriya ta ƙi cewa uffan game da sabon harin da yahallaka mutane da dama a ranar bikin Easter a garin Kaduna dake sashen arewacin kasar

An dai kai ga jerin alkawura dama ziyarar bayan hare-hare. An kuma shayin Allah wadai dama alkawarin ganin bayan matsalar.

To sai dai kuma daga dukkan alamu tana neman wucewa da sanin fadar shugaban Najeriya da a karon farko ta zura ido tana kallon ikon Allah game da sabon harin ranar bikin Easter na mabiya addini kirista a garin Kaduna dake arewacin kasar

Harin kuma da aka zaci faruwarsa a wani bangaren kasar sannan kuma ke ci gaba da tada hakarkari a tsakanin al'ummar kasar.

Akalla mutane 38 ne dai aka tabbatar da labarin rasuwar su, sakamakon bomb din na Kaduna dake zaman hari na uku mafi girma tun bayan kaddamar da hare haren da ke neman zama rowan dare a kasar.

©Jonathan Rebboah/Wostok Press/Maxppp France, Paris 25/11/2011 Le president du Nigeria Goodluck Jonathan arrive au palais de l Elysee The President of Nigeria Goodluck Jonathan at the Elysee Palace
Goodluck Jonathan shugaban NajeriyaHoto: picture alliance / dpa

Gwamnati ta yi gum

Fadar gwamantin kasar da kan yi saurin Allah wadai dama ikirarin daukar mataki, a duk lokacin da makamancin wannan harin ya faru, amma a abun mamaki babu wani jami'in gwamnati da aka ji bakinsa. Haka ita ma dai kungiyar kiristocin kasar ta CAN ba tace uffan ba game da harin da ake kyautata zaton na da burin jiwa masu bikin na Easter da kuma aka kaddamar da shi a gefen wata coci.

Majiyoyin fadar gwamantin dai sun ce shugaba Jonathan ya gaji da shan alwashi yana rushewa ga batun shawo kan matsalar tsaron dake neman gagarar kundilar kasar ta Najeriya.

To sai dai kuma sabon harin da jami'an tsaron kasar ta Najeriya suka yi gargardin yiwuwar sa can a birnin Kano da kuma ya zo yan sa'o'i da alwashin shugaban Najeriya na nuna irin jan aikin da yanzu haka ke gaban yan siyasa dama jami'an tsaron kasar ta Najeriya, na tunkarar annobar tsaron dake neman aure ta tare cikin kasar.

epa03026909 Nigerian police control a street shortly after a bomb blast in a market in Ogbomoshoin area of Kaduna, Nigeria, 07 December 2011. Reports state the early morning explosion in the northern city of Kaduna killed 10 people, including a pregnant woman and two children. A group suspected to be Islamist militants reportedly arrived on motorbikes and threw bombs into the crowded spare parts market. EPA/STR +++(c) dpa - Bildfunk+++
Jama'ar da suka taru bayan harin KadunaHoto: picture-alliance/dpa

Shi kansa karatun kurmar fadar game da harin a cewar Garba Umar Kari dake zaman masanin harkokin zamantakewa a jamiar babban birnin Tarayya dake Abuja na nuna irin koma bayan da gwamnatin ke fuskanta ga yakin da ke neman cika shekara guda kuma ke tada hankula a ciki dama wajen kasar.

"Har ya zuwa yammacin Lahdi ranar da aka kai harin babu wata ƙungiyar da ta fito domin daukar nauyin harin da ya yi kama da wani dan uwansa da aka kai garin Madalla na jihar Niger a ranar bikin kirsimatin bara"

Zamantakewar addinai a Najeriya

Akwai dai tsoron yiwuwar amfani da irin wadannan hare-hare a matsayin damar rikicin addinin a kasar ta Najeriya dake rabe tsakanin mabiyan manyan addinan kasar biyu da kuma a baya aka sha fafatawa kan banbance-banbance a tsakanin bangarorin biyu.

Duk da cewar dai hakarkari ya kai ga dagawa dama nuna yatsa a tsakanin shugabanin dake jan ragamar harkokin addinan Najeriya, ya zuwa yanzu dai kasar ta kai ga tsallake tarkon rikicin addini da a baya ya kai ga hallakar duban yan kasar da kuma barazana ga makomar ta.

Thousands of people attend the Redeemed Christian Church Of God holy ghost all night revivals at the church camp in Lagos,Nigeria Friday, Feb. 3, 2006.(AP Photo/George Osodi)
Wasu al'umma ke addo'a cikin wata mujami'aHoto: AP

To sai dai kuma a cewar Mallam Kari sababbin bama-bamai dama rawar yan siyasa da jami'an tsaron Tarrayar ta Najeriya na daɗa haifar da rashin tabbas a zukatan al'ummar kasar dake fatan ganin karshen matsalar a cikin sauri.

Sama da mutune 800 ne dai suka rasu a cikin wattani 4 na farkon wannan shekara da muke ciki, sakamakon hare haren da ake ta'allkawa da ayyukan yayan kungiyar boko haram, kamar dai yadda alƙaluma ididdiga suka bayyana.

Mawallafi: Ubale Musa

Edita: Usman Shehu Usman

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani