Zaben Najeriya: An soma bayyana sakamon zabe a wasu Jihohin
February 23, 2019Talla
Rahotanni sun tabbatar da cewar a wasu jihohin Najeriyar an soma kidayar kur'i'u. Tun farko dai wata kungiyar masu saka ido a shafinta na Twitter, ta ce an samu tsaiko bisa rashin isowar jami'an hukumar zaben da kuma matsaloli na ko rashin aikin na'aurar tantance bayanai ta card reader da tambari da dai sauransu. Jihohin da aka samu wadannan matsalolin sun hada da Akwa Ibom da ke kudancin kasar da kuma Legas, birni mafi girma a Najeriyan har ma da Jihar Kano.