1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yemen: MDD ta soki Saudiyya da kawayenta

Zulaiha Abubakar
August 25, 2018

Hukumar bada agajin gaggawa ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da hare-haren da kasar Saudiyya ke ci gaba da jagoranta a Yemen, wadanda ke janyo rasa rayukan fararen hula da suka hada da mata da kananan yara.

https://p.dw.com/p/33jlP
Jemen Beerdigung von Opfern eines Luftangriffs in Saada
Hoto: Reuters/N. Rahma

Rikicin kasar ta Yemen ya fara ne a shekara ta 2014 yayin da 'yan tawayen Houthi mabiya darikar Shi'a suka karbe birnin Sanaa bayan hambarar da gwamnati, lamarin da kasar Saudiyya tare da kawayen da daga cikin kasashen Larabawa suka lashi takobin sai sun ga bayan sa. Hukumar agajin gaggawar ta ja hankalin Majalisar Dinkin Duniya kan ta gaggauta gudanar da bincike.