Babu wasan sada zumunta tsakanin Isra'ilada Argentina
June 6, 2018Talla
An dai soke wasan na sada zumunta a kan matsin lambar da Faladinawa suka yi a kan Lionel Messi cewar kada ya shiga wasan,domin martaba dubban magoya bayansa falasdinawa musulmi, wanda Isra'ila ke yi wa kashin mumuke kamar yadda suka bayyana. Ministan tsaro na Isra'ila Avigdor Lieberman, ya rubuta a shafinsa na Twitter cewar soke wasan abin takaici ne.