1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kare muhalli kwalliya ta biya kudin sabulu

December 12, 2020

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga kasashen duniya da su saka dokar tabaci kan dumamar yanayi a kasashensu.

https://p.dw.com/p/3mdHi
UN-Generalsekretär  Antonio Guterres
Hoto: picture-alliance/ Pacific Press/L. Radin

A wajen wani kasaitaccen bukin cika shekaru biyar da kasashen duniya su ka shiga yarjejeniya kan dumamar yanayi a Birnin Paris na kasar Faransa, Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres ya bukaci kasashen duniya da su kakaba dokar tabaci domin yaki da dumamar yanayi a kasashensu. 

Masana a fadin duniya sun ce an samu saukin dumamar yanayi a duniya, tun bayan shiga yarjejeniya kan dumamar yanayi shekaru biyar din da suka gabata.

Sai dai masanan sun ce ambaliyar ruwan da aka samu a kasashen yammaci da gabashin Nahiyar Afirka a bana, da gobarar daji a Ostareliya da kuma iska mai karfi a yanki Amirka na nuni da cewa akwai sauran gagarumin aiki a gaba.

Kasahen Italiya da Birtaniya da Faransa da kuma Majalisar Dinkin Duniya sune suka shirya bukin na yau, da ya samu halartar kasashe sama da saba'in na duniya, amma ta kafar bidiyo.