1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu Kwoyelo da laifin cin zarafin jama'a a Yuganda

Zainab Mohammed Abubakar
August 13, 2024

Kotu ta samu wani tsohon kwamandan kungiyar ‘yan tawayen ta LRA da laifukan cin zarafin bil’adama, a wani muhimmin shari’a ga mutane da suka sha azabar fadan 'yan tawaye a Yuganda.

https://p.dw.com/p/4jQki
Thomas KwoyeloHoto: GAEL GRILHOT/AFP

Wani kwamitin babban kotun da ke zama a Gulu, da ke arewacin kasar ya tabbatar da laifukan da aka dade ana jira a shari'ar Thomas Kwoyelo. Wannan dai shi ne hukuncin ta'addanci na farko da aka yi shari'arsa, a karkashin wani bangare na musamman na babbar kotun da ke shari'ar manyan laifukan na kasa da kasa.

Kwoyelo ya fuskanci tuhume-tuhume da suka hada da kisan kai, sata, bautar da mutane, dauri, fyade da zalunci. An yanke masa hukunci kan tuhume-tuhume 44 daga cikin 78 da ya aikata tsakanin shekarar 1992 zuwa 2005.

Kwoyelo, wanda aka fara shari'ar sa a shekarar 2019, yana tsare tun 2009 yayin da hukumomin Yuganda suka yi kokarin gano yadda za a gudanar da adalci ta hanyar da ta dace da gaskiya.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta bayyana shari'ar tasa a matsayin "wata dama ce da-ba-kasafai ake samunta ba na yin adalci ga wadanda aka kashe a yakin shekaru 20 tsakanin" sojojin Yuganda da Kungiyar tawayen ta LRA.