An sami nasarar taron duniya kan Somaliya a London
May 10, 2013A wannan ako, shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou ya ziyarci Jamus, inda ya gana da shugabanni, tare da nazarin dangantakar siyasa da tattalin arziki da kuma hadin kan taimakon raya kasa. Jaridar Neues Deutschland tayi amfani da wannan dama, domin duba halin da mazauna yankin arewacin kasar ta Nijar suke ciki, sakamakon gurbacewar yanayi saboda hakar ma'adinai, musamman sinadarin Uranium. Kungiyoyin kare hakkin jama'a sun tashi tsaye domin gwagwarmaya da kamfanin Faransa mai suna AREVA da kamfanin China mai suna Somina dake hakar Uranium tare da gurbata muhalli a arewacin Nijar din. Jaridar tayi tsokaci da cewar kungiyoyin na farar hula suna korafi ne saboda gurbacewar ruwan sha da kasar noma, abin dake haddasa illa ga rayuwar jama'a da dabbobi. Ma'aikata a wadannan kamfanoni kuma, suna neman kyautata sharuddan aikinsu, da basu yanci da hakkin da basu dashi yanzu a bakin aikinsu. Yayin da shugabannin kamfanin na hakar Uranium suka ki cewa komai a game da waannan zargi, gwamnati a Yamai tana kokarin shirya ganawar sulhu tsakanin shugabannin kamfanonin da kungiyoyin ma'aikata.
Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung ta duba taron da aka yi ne a wannan mako kan kasar Somaliya a London, inda ma ta nunar da cewar mahalarta taron sun yi marhabin da irin ci gaban da ake samun a matakan kyautata zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar ta Somaliya. Wannan taro ya zama wajibi, inji Pirayim ministan Britanniya, David Cameron a jawabinsa gaban wakilan kasashe da kungiyoyin duniya. Fiye da kashi biyu cikin kashi ukku na al'umar Somaliya gaba daya, matasa ne da basu wuce shekaru 25 da haihuwa ba, inda mafi yawansu suke rayuwa da abin da bai kai dolla daya ba a rana. Mahalarta taron gaba daya, inji jaridar Neue Zürcher Zeitung, bakinsu yazo daya a sanarwar karshe cewar sabuwar zababbiyar gwamnatin Hassan Sheikh Mohammed ta sami ci gaba a kokarinta na tabbatar da tsaro da shimfida democradiya da ci gaban kasar ta fuskar tatalin arziki.
Al'ummar kasarmu bai kamata su ci agaba da rayuwa cikin mummunan hali ba. Wannan dai shine taken da jaridar Die Tageszeitung tayi amfani dashi, domin maimaita kalamomin shugaban jam'iyar adawa ta Angola, wato Unita, Isaias Samakuva, lokacin da yake korafin gibin dake karuwa a tsakanin masu hannu da shuni da matalauta a wannan kasa. Jaridar tace Angola dai tana daya daga cikin kasashen da suka fi arzikin man fetur da kuma sayar dashi a nahiyar Afirka, kuma tana samun dolla miliyoyi dubbai daga wannan arziki nata, to sai dai kasar ta kasance a wani yanayi ne na tsaka-mai-wuya. Saboda hakan ne Samakakuva yayi gargadin yiwuwar samun juyin juya hali, muddin matasa suka hau kan tituna domin baiyana kara game da mummunan matsayin da suke ciki.
Halin da ake ciki na rashin kwanciyar hankali a kudancin Sudan yana ci gaba da daukar hankalin jaridu a nan Jamus. Jaridar Neues Deutschland tace gwamnatin Sudan ta arewa a birnin Khartoum tana kara fama da matsin lamba bayan da hadin gwiwar wasu kungiyoyi na yan tawaye a makon jiya suka kai hari kan dakarun gwamnatin a lardin Kudancin Kordofan. Saboda haka ma shugaban daya daga cikin wadannan kungiyyi, Yasir Arman yace yanzu dai yaki a barke kai tsaye a kudancin Sudan. Dan tawayen yace shi da sauran kungiyoyi abokansa tuni ma suka kwace wani yanki na Kudancin Sudan din, suka maida shi karkashin ikonsu. Yankin Kudancin Kordofan yaci gaba da zama karkashin ikon gwamnatin birnin Khartoum, ko ma bayan da yankin kudancin Sudan ya balle, ya ma zama mai mulkin kansa a shekara ta 2011.