1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake kiran wata sabuwar zanga- zanga a Chadi

April 30, 2021

Hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane sama dari bakwai ne yanzu haka ake tsare da su a Chadi.

https://p.dw.com/p/3sopX
Tschad N'Djamena | Proteste und Gewalt
Hoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Kamen ya biyo bayan zanga-zangar adawa da matakin majalisar sojin kasar ta dauka na nada Muhamat Idriss Deby a matsayin shugaban kasar bayan rasuwar mahaifinsa.

Mai magana da yawun hukumar ta yankin  Marta Hurtado ta ce ba su da takamaimai alkalunman adadin mutanen da ake tsare  dasu, amma dai sun san mutanen sun zarta adadin da aka ambata. Sai dai kungiyoyin fararen hula a Chadin sun sake kiran wata sabuwar zanga-zangar a ranekun hutun karshen mako na Asabar da Lahadi.

Dama tun a zanga-zangar da aka fara ranar Talata, an zargi jami'an tsaro da yin amfani da harsashin gaske tare da hallaka akalla mutane biyar, lamarin hukumomin kare hakkin dan Adam na ciki da wajen kasar da kuma kasashen duniya cikinsu har da uwar gijiyarta ta Faransa suka yi Allah wadai da shi.