1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

A watan Febrairu za a yi zaben Jamus

Suleiman Babayo ATB
November 12, 2024

Manyan jam'iyyun siyasa na Jamus sun amince da saka watan Febrairu mai zuwa ta 2025 domin zaben kasa baki daya a Jamus bayan rushewar gwamnatin kawance da shugaban gwamnatin Okaf Scholz yake jagoranci.

https://p.dw.com/p/4mvHi
Jamus | Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf ScholzHoto: Fabian Sommer/dpa/picture alliance

Bayan rushewar gwamnatin kawancen Jamus an saka ranar 23 ga watan Febrairun shekara mai zuwa ta 2025 domin gudanar da zaben gama-gari a kasar. Kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA ya ruwaito a wannan Talata cewa manyan jam'iyyun siyasa na kasar suka amince da haka, bayan jam'iyyar da take mulki ta SPD ta cimma matsaya da babbar jam'iyyar adawa ta CDU.

Yanzu ana sa ran ranar 16 ga watan gobe na Disamba shugaban gwamnati Olaf Scholz zai bukaci majalisar dokoki ta Bundestag ta kada kuri'ar yanke kauna ga gwamnatinsa. Bayan kuri'ar daga bisani shugaban kasar Frank-Walter Steinmeier zai bukaci gudanar da zabe cikin gwamnati 60 kamar yadda dokokin Jamus suka tanada.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya rasa rinjaye da yake da shi a majalisar dokoki karkashin kawancen jam'iyyun uku, bayan jam'iyyar FDP mai ra'ayin jari hujja ta fice daga cikin kawance sakamakon sabani kan kasanin kudi na shekara ta 2025.