An saka ranar zabe a Yuganda
November 4, 2020Hukumar zaben kasar Yuganda ta tabbatar da zaben kasar na ranar 14 ga watan Janairu mai zuwa na shekara ta 2021, inda za a fafata tsakanin Shugaba Yoweri Museveni da matashi mawaki mai farin jini Bobi Wine, inda a gaba daya akwai 'yan takara 11.
Mai magana da yawun hukumar zaben ya saka a shafinsa na sada zumunta na Tuwita cewa an gayyaci 'yan takara zuwa hukumar zaben a wannan Alhamis domin tattauna harkokin zaben.
Shugaba Yoweri Museveni da ke da shekaru 76 da haihuwa, wanda ya kwaci da madafun ikon kasar ta Yuganda tun shekarar 1986 ta hanyar tawaye, ya yi ta gyara ga kundin tsarin mulkin domin samun tazarce, yayin da a daya bangaren mawaki Bobi Wine, wanda asalin sunansa shi ne Robert Kyagulanyi dan majalisar dokoki da ke da shekaru 38 da haihuwa, ya yi suna saboda neman ganin an samar da tsarin kwatanta gaskiya da adalci da yaki da cin hanci da talauci.