1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sace malaman jinya a Zaria ta Najeriya

July 5, 2021

Akalla ma'aikatan jinya takwas ne masu garkuwa da mutane suka sace a garin Zaria ta jihar Kaduna bayan da suka afka wa wasu cibiyoyin kiwon lafiya a arewacin Najeriya.

https://p.dw.com/p/3w1pq
Nigeria Abuja | Sicherheitspersonal | Entführte Studenten
Hoto: Nasu Bori/AFP/Getty Images

A wani sabon hari da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa suka kaddamar a wata asibitin kutare da masu fama da tarin fuka ko TB, an yi awon gaba da malaman jinya a birnin Zaria na jihar Kaduna.  Kawo yanzu ba bu tabbacin takamaiman adadin wadanda aka dauke, sai dai wata majiya ta ce mutane takwas ne abin ya rutsa dasu, yayin da wata majiyar kuma ta bayyana cewar mutanen da aka yi garkuwa da su sun kai goma sha biyar.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kaduna a Arewa maso yammacin Najeriya Mohammed Jalige ya tabbatar da sace ma'aikatan bayan wata misayar wuta da 'yan sandan suka yi da 'yan ta'adan.

Sace-sacen mutane don neman kudin fansa na neman zama ruwan dare musmman ma a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da ke arewacin tarayyar Najeriya.