SiyasaTurai
Jagoran adawar Rasha ya sha guba
August 20, 2020Talla
Rahotanni daga asibitin da aka kwantar da shi a birnin Omsk na kasar Rasha sun ce kawo yanzu ana zargin jagoran adawar na Rasha ya hadiyi guba ne, a wani lamari da ke da matukar daure kai.
Bayanan da DW ta samu na nuni cewa Alexei Navalny ya shiga cikin yanayin rai-kwakwai-mutu-kwakwai, inda aka ce an sanya masa na'urar taimaka wa numfashi domin ya samu ya murmure. Gwamnatin Rasha dai ba da jimawa ba ta sanar da cewa tana yi wa jagoran adawar fatan alheri, yayin da kungiyar tarayyar Turai ta EU ta ce ta kadu matuka da wannan labari.