1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nemi 'yan Mali su yi zanga-zanga a yau

January 14, 2022

Gwamnatin mulkin sojin Mali ta nemi 'yan kasar da su fantsama kan tituna domin gudanar da zanga-zangar adawa da matakin da Kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta dauka na sanya mata takunkumi saboda dage zaben gama-gar

https://p.dw.com/p/45WKu
Weltspiegel | Bamako, Mali | Militärputsch, Protest gegen Frankreich
Hoto: Michele Cattani/AFP

Shugaban gwamnatin mulkin sojin Mali din en ya bukaci a yi zanga-zangar a wanann Juma'ar don nunawa ECOWAS cewar ba su amince da takunkumin da aka sanya musu ba saboda jingine zaben gama-gari na watan Fabrairu da suka yi alkawarin kafin daga bisani su jingine shi.

Wannan zanga-zanga ta yau dau na zuwa ne daidai loakcin da babban sakataren majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce akwai bukatar sojojin su fitar da gamsashen jadawalin zabe, kana ya ce ya gana da shugabanin kasashen Ghana da Senegal da na Najeriya da kuma shugaban kungiyar Tarayyar Afirka, tare da fatan tuntubar gwamnatin Mali kan batun jinkirta zabe.