1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Xi Jinping

November 15, 2012

Jam'iyyar kominisanci ta China a babban taronta ta nada Xi Jinping a matsayin sabon shugabanta, inda hakan ta sanya shi a matsayin wanda zai gaji Shugaba Hu Jintao.To ko wa nene Xi Jinping?

https://p.dw.com/p/16jlM
Hoto: Reuters

Shi dai Xi Jinping mutun ne da bai shahara sosai ba a siyasar kasar ta China ko da yake an san shi a matsayin mijin Peng Liyuan shahararrriyar mawakiyar nan ta China da ta yi tashe da wakenta masu suna "Kasar Mahaifina" da "Gaba gaba dai Kasar China." A hakika Xi ya yi suna ne da sunan matarsa.

Xi ya fito ne daga tsatson gwarzo

Wani bayanin sirri da shafin yanar gizo na Wikileaks ya watsa akan ofishin jakadanci Amirka ya bayyanar da shi tamkar mutun mai cike da buri samun daukaka. Shi dai Xi wanda mahaifinsa daya ne daga cikin gwarzayen da suka jagorancin juyin -juyahalin kasar China an haife shi ne a shekarar 1953. Ya kuma girma ne a sosomin mulkin komnisanci na kasar. Masu sa ido akan yadda jam'iyyar ta Kominis ke tafiyar da al'amuranta suna daukarsa tamkar daya daga cikin magadan kusoshin jam'iyyar. A farko shekarun 1960 ne dai aka samu mahaifinsa da laifi cin amanar jam'iyyar a wani mataki na yin tankade da rairaya a cikin jam'iyyar dalilin da ya sa ya shafe shekaru yana zanue a gidan yari. To amma sai aka nuna masa sassuci bayan mutuwar Mao. Shi dai mahaifin Xi ya yi aiki na wani dan lokaci a matsayin gwamnan jihar Guandong a lokacin mulkin Deng Xiaoping.

Xi Jinping na zaman daya daga cikin miliyoyin matasa da aka tura zuwa yankin karkara a lokacin juyin juya juya al'adun kasar ta China-dalilin da ya sa ya shafe shekaru yana zaune al lardin Schaanxi da ke kuryar kasar. To amma ya dawo birnin Peking inda ya shiga jam'iyyar Kominis domin cimma burinsa na siyasa a daidai lokacin da shi mahaifin nasa ke gidan yari. Daga nan ne kuma ya shiga aikin soja inda ya zamo mataimakin ministan tsaro, Geng Biao. Daga bisani ya rike mukamin sakataren jam'iyyar kuma gwamnan lardunan Zhejiang da Fujian da ke gabar tekun China. A shekarar 2007 ne dai ya zama daya daga cikin masu ruwa da tsaki a fannin shugabancin kasar.

China's Vice President Xi Jinping (front L) and China's Vice-Premier Li Keqiang (front R) leave their seats after the closing session of 18th National Congress of the Communist Party of China at the Great Hall of the People in Beijing, November 14, 2012. China's Communist Party congress offered the first clues on a generational leadership change on Wednesday as Xi Jinping and Li Keqiang took the first step to the presidency and premiership, respectively. The 2,270 carefully vetted delegates cast their votes behind closed doors in Beijing's cavernous Great Hall of the People for the new Central Committee, a ruling council with around 200 full members and 170 or so alternate members with no voting rights. REUTERS/Jason Lee (CHINA - Tags: POLITICS)
Xi Jinping da Li Keqiang, mataimakin firaiministanHoto: Reuters

Kasashen yamma sun yi madallah da Xi

Xi mutun ne da kasashen yamma ke daukarsa a matsayin mai saukin kai. 'Yarsa ta ma yi karatu ne a jami'ar Havard da ke Amirka inda shi kansa ya sha yin balaguro. Ya kuma san zargi- zargin da kasashen yamma ke wa kasarsa da kuma abin da ake sa ran ji a kasar tasa da ya hada da batun kasuwanci da kare hakkin bil Adama. Yayin wata ziyara da ya kai Amirka ya ba da mamaki game da kalaman da ya yi game da kare hakkin bil Adama a China. Ya ce:

Image #: 16915169 U.S. President Barack Obama meets with Chinese Vice President Xi Jinping in the Oval Office at the White House in Washington on February 14, 2012. UPI/Kevin Dietsch /LANDOV pixel
Xi Jinping da Barack Obama a fadar White HouseHoto: picture alliance/landov

"Ina jadadda muku cewa kasar China ta samu gagarumin ci gaba a fannin kare hakkin bil Adama a shekaru 30 da suka gabata. Zan iya cewa an samu kwarya-kwaryar ci gaba. Ita dai gwamnatin China har yanzu tana fuskantar kalubale wajen samar da inganci a fannin kare hakkin bil Adama da kuma jin dadin rayuwar al'uma .

A matsayin yanki na wannan ziyara tasa ya kuma ya da zango a kasar Mexico inda yayi suka ga kasashen yamma kamar haka:

"Akwai wasu kasahen ketare da ke sukan lamirin mu alhalin kuwa su kansu ba su tsere mana ba wajen yin wani abin azo a gani .Na farko China bata daukar matakin samar da sauyi a ketare. Na biyu China ba ta aike yunwa da talauci zuwa ketare. Kuma na uku China ba ta katsalanda a harkokin ketare. To wai me nene suke bukata ?

Za ku iya sauraron sautin wannan rahoto daga kasa.

Mawallafi: Mathias Boelinger/ Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammed Nasir Awal