ICC: Za ta tuhumi jagoran 'yan tawaye Alfred Yekatom
November 17, 2018Yekatom ya kasance mutumin da ake zargi da aikata laifukan yaki da keta haddin dan Adam, shi ne kuma mutum na farko da kasar da ke fama da rigingimun kabilanci da addini, ta mika kotun ICC da aka samar da zummar hukunta masu ire-iren wadannan laifuka.
Za a tuhumi Yekatom bisa laifin jagorantar kisan musulmai da fararen hula da kuma tilasta wa yara sama da 100 shiga aikin soja a yayin rikicin da ya lakume rayuka a rikicin Afirka ta Tsakiya. A shekarar 2016, aka zabi Yekatom a matsayin wakili a majalisar kasar, sai dai an kama shi a watan Oktoba, bayan da ya bude wuta a zauren majalisa a yayin da shugaban majalisar ke shirin gabatar da jawabinsa na farko bayan da aka zabe shi.
A sanarwar gwamnati ta ce wannan mataki ne na aika sako cewa da gaske ta ke a hukunta duk wadanda suka janyo wa kasar asarar rayuka da dukiyoyi.