An kuma samun mai Ebola a Amirka
October 24, 2014Likitan wanda ke aiki da Ƙungiyar "Doctors Without Borders" Dr. Craig Spencer ya kula da masu ɗauke da cutar ta Ebola a ƙasar Gini gabanin dawowarsa birnin New York ɗin Amirkan. Magajin garin birnin na New York Bill de Blasio ya nemi al'ummar birnin da su kwantar da hankulansu, kasancewar Dr. Spencer ya yi ziyarce-ziyarce ta hanyar amfani da ababen hawa na al'umma gabanin tabbatar da cewar ya na ɗauke da Ebola. A yanzu haka dai Spencer na zaman mutum na huɗu a Amirka da ya kamu da wannan cuta tun bayan da mutum na farko dan asaklin ƙasar Laberiya ya kai musu tsarabarta. Tuni dai Shugaba Barack Obama na Amirkan ya ce gwamnati za ta ba da dukkan taimakon da birnin na New York ke buƙata domin daƙile yaduwar cutar dama kula da likitan da ya kamu da ita.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane