1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe sojojin Chadi 8 a fafatawa da Boko Haram

Mohammad Nasiru Awal AS
June 26, 2017

Hakan ya zo ne a daidai lokacin da Shugaba Deby ya ce rashin kudi ka iya tilasta janye dakarun kasar daga yaki da ta'adda.

https://p.dw.com/p/2fPLV
Soldaten aus dem Tschad
Hoto: AFP/Getty Images/M. Medina

Sojojin Chadi takwas ne aka kashe sannan aka ji wa 18 rauni a wani kazamin fada da suka yi da mayakan Boko Haram a karshen mako a wasu tsibarai da ke tafkin Chadi da ke kan iyaka da kasashe hudu na dab da hamadar Sahara.

Kakakin rundunar sojin Chadi Kanal Azem ya fada a wannan Litinin cewa dakarun kasar sun kai hari kan mayakan Boko Haram a tsibirai guda biyar da ke kusa da Najeriya a rainakin 24 da 25 ga watannan na Yuni, yana mai cewa sun yi asarar sojoji takwas sannan 18 sun jikkata. Ya kuma yi ikirarin cewa dakarun Chadi sun kashe 'yan Boko Haram 162.

A wani labarin kuma Shugaba Idris Deby na Chadi da ke zama babban abokin kasashen yamma a yaki da masu tsattsauran ra'ayin addini, ya ce rashin kudi ka iya tilasta wa Chadin janye wasu daga cikin dakarunta a yakin da ake yi da 'yan ta'adda, matukar ba ta samu taimakon kudi ba.