1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan kawance sun kashe dubban 'yan Houthi

Zainab Mohammed Abubakar
November 18, 2021

Majiyar kusa da mayakan tawayen Houthi ta tabbatar da kisan mayakansu kusan dubu 15 a Yemen a kusa da birnin Marib mai arzikin mai.

https://p.dw.com/p/43Cnw
Jemen | Kämpfer gegen die Huthi-Rebellen nahe Marib
Hoto: Nariman El-Mofty/AP Photo/picture alliance

Marib dai na zama yanki na karshe mai muhimmanci da ke karkashin ikon gwamnati kuma mai arzikin mai a yankin arewacin Yemen.

A bara nedai mayakan na Houthi da ke samun goyon bayan Iran suka yi kokarin karbe madafan ikon birnin. Duk da cewar an samu tsaiko saboda kokarin sasantawa, mayakan tawayen sun sake sabunta hare harensu a watannin Febrairu da Yuni da Satumba.

Mayakan kawance karkashin jagorancin Saudi Arabiya wadanda suka afkawa kasar a wani mataki na goyon bayan gwamnati, na ci gaba da ayyana nasarar murkushe 'yan Houthi a kewayen Marib tun daga ranar 11 ga watan Oktoba.