Human Rights na zargin Taliban da kisan jami'an tsaro
November 30, 2021A wani sabon rahoto da Human Rights Watch ta fitar a wannan Talata, ta ce Taliban ta kashe ko kuma tayi sanadiyar bacewar jami'an tsaro na tsohuwar gwamnatin Afghanistan da ta hambarar, a rahoton hukumar da ke kare hakkin dan Adam a duniya, mai shafi ashirin da biyar, ta ce jami'an tsaro fiye da dari, rahoton ya gano aka halaka ko kuma suka yi batan dabo, tun bayan da Taliban din ta kwace mulki a watan Augustan da ya gabata.
Human Rights Watch ta zargi masu rike da madafun ikon Afghanistan da yin amfani da wasu bayanai na tsohuwar gwamnatin don gano mutanen da ta ce, an kama kafin aiwatar da kisan bayan da aka azabtar da su.
Kawo yanzu Taliban ba ta kai ga mayar da martani ba kan wannan sabon rahoto da ke zuwa a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da fuskantar tashin hankali. Ko a safiyar wannan Talata, an kai wani harin bam a Kabul babban birnin kasar inda aka tafka asarar da mahukunta suka ce ba su kai ga tantance adadinta ba.