An kara tsananta matakan tsaro a birnin London
June 30, 2007Talla
´Yan sanda a London babban birnin kasar Birtaniya sun tsananta binciken da suke yi don gano wadanda ke da hannu a yunkuri kai harin bam a birnin. Rahotanni daga London sun ce yanzu an fara tuntubar hukumomin wasu kasashen waje a cikin binciken. A dai halin da ake ciki an tsaurara matakan tsaro inda kuma ´yan sanda suka tsananta binciken ababan hawa a birnin. Kwararrun masana harkokin tsaro sun ce shirin kai hare haren na da kama da aikin kungiyar ´yan ta´adda ta al-Qaida.