1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala taron G20 cikin saɓanin ra'ayoyi

Regina BrinkmannSeptember 6, 2013

Shugabannin ƙasashen duniya sun gaza cimma matsa ɗaya a kan rikicin ƙasar Siriya wanda Amirka ke son yin amfani da ƙarfin soji a taron St Petersburg na Rasha.

https://p.dw.com/p/19dIT
PETERSBURG, RUSSIA - SEPTEMBER 06: In this handout image provided by Host Photo Agency, a general view is pictured during the second working meeting of the G20 heads of state and government, heads of invited states and international organizations at the G20 Summit on September 6, 2013 in St. Petersburg, Russia. Leaders of the G20 nations made progress on tightening up on multinational company tax avoidance, but remain divided over the Syrian conflict as they enter the final day of the Russian summit. (Photo by Alexei Danichev/Host Photo Agency via Getty Images)
Hoto: Alexei Danichev/Host Photo Agency/Getty Images

An watse baram-baram a taron ƙasashen masu ƙarfin tattalin arzki masana'antu na duniya wato G20 tare da gasa warware saɓanin da ke tsakanin Amirka da Rasha a kan yunƙurin shugaba Barack Obama na yin amfanin da ƙarfin soji a kan Siriya wacce yake zargi da yin amfani makamai masu guba a yakin da take yi da ' yan tawaye.

Tun daga daran jiya har yazuwa yau Juma'a da aka kammala taron shugabannin ƙasashen duniyar guda 20 ke ta tafka mahawara a kan batun wanda ra'oyoyi suka bambanta. Bayan tattaunawar kuma da aka kwashe mintoci 20 ana yi tsakanin Obama da Putin wacce ba ta kawo ƙarshen rarrabuwar kawunan da ke tsakanin ƙasashen ba.

Saɓani ya fito fili tsakanin Rasha da Amirka a kan batun Siriya

Amirka dai na zargin hukumomin Siriya da cewar sune ke da alhakin kai harin makamai masu guba da aka kai a ranar 21 ga watan Augusta da ya wucce a kusa da Damascus wanda a ciki mutane dubu ɗaya da ɗari fuɗu suka mutu.To amma shugaba Vladimir Putin na Rasha na mai cewar ' yan tawayen na Siriya sune suka kitsa harin. Sai dai duk da gargaɗin da babban sakataran MDD Ban Ki Moon ya yi cewar kai farmakin zai haifar da mumunar sakamako shugaba Barack Obama ya dage a kan matsayinsa.

U.S. President Barack Obama (2nd L) listens as President Xi Jinping of China (R) speaks during their meeting at the G20 Summit in St. Petersburg, Russia September 6, 2013. REUTERS/Kevin Lamarque (RUSSIA - Tags: POLITICS)
Zauren taron na G20Hoto: Reuters

Ya ce:''Babu wata ammsa a wannan karya doka ta ƙasa da ƙasa da Siriya ta yi kuma duniya ba za ta zuba ido ba ta kalli wannan keta hadi kasashe da dama sun amince da a mayar da martani.''

Putine dai ya ce yana akan matsayinsa babu gudu babu ja da baya ya ce suna taimaka Siriya kuma zasu ci gaba da taimakamata tare da bayyana cewar tuni da suka aike da wani jirgin ruwan yaƙi a tekun Mediterraneen kana kuma ya ƙara da cewar.

Ya ce: ''Ina tabbatar muku da cewar hasashe na ƙarshe na nuna cewar yawancin ƙasahen duniyar kishi 60 zuwa 70 cikin ɗari na tare da mu saboda ba su goyon bayan a kai farmakin.''

Yunƙurin sauran ƙasashen duniya na ganin a warware rikicin ta hanyar diflomasiya

Haka dai aka watse hannu riga ba tare da samu daidaituwar baki ba tsakanin shugabannin, kuma ko da shi ke ɗaya daga cikin shugabannin da ke goyon bayan Barack Obama wato Francois Hollande na Faransa ya ce ƙasarsa za ta jira sakamakon binciken sefetocin MDD shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi gargaɗin cewar har yanzu a kwai sauran dama ta shirya wani taro na ƙasa da ƙasa domin samar da hanyoyin sulhu na diflomasiya don warware rikicin.

Frances President Francois Hollande (L) smiles while talking to Germanys Chancellor Angela Merkel as they attend a meeting with Business 20 and Labour 20 representatives during the G20 summit on September 6, 2013 in Saint Petersburg. AFP PHOTO / ERIC FEFERBERG (Photo credit should read ERIC FEFERBERG/AFP/Getty Images)
Angela Merkel da Francois HollandeHoto: Eric Feferberg/AFP/Getty Images

Ta ce:''Mahawarar tana da mahimanci ya kamata a samu canji, a kwai tunani na wakilai da dama na bin hanyoyin sulhun, ina tsamanin ƙasahe irinsu Rasha da China za su iya ba da tasu gudumowa don ganin an shirya wani taro a Jeniva.''

Yanzu haka dai duniya ta zura ido ta yadda za a gaya a kan wannan batu mai sarƙaƙiya na Siriya bayan kammala taron na ƙasashe guda 20 masu ƙarfin arzikin masana'antu na duniya ba tare da cimma nasarar samun bakin zaren rikicin ba.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da rahoton da wakilinmu na ƙasar Masar Mahamud Azare Yaya ya aiko mana akan lamarin na Siriya.

Mawallafi Abdourahamane Hassane

Edita : Umaru Aliyu

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani