An fara kame masu hannu da kisan dalibai
October 30, 2015Talla
An dai kama magajin garin na Cocula Erick Ulises Ramirez ne tare da shugaban gungun da ake zargi da sace daliban mai suna Adan Casarrubias. Daliban su 43 sun yi batan dabo ne kafin daga bisani a gano gawarwakinsu a birnin na Cocula . Rahotanni sun bayyana cewa an cafke shugaban gungun mutane da ake zargi da sace daliban tare da kashe su ne yayin wani samamen hadin gwiwa tsakanin jami'an 'yan sanda da sojojin kasar a Larabar da ta gabata a birnin Cuernavaca da ke jihar Morelos. An kuma kame wani da aka ce mai bayar da shawara ta fannin shari'a ne ga jam'iyyar masu ra'ayin rikau ta Democratic Revolution (PRD), wanda shima ake zargi da hannu a wannan aika-aika.