An kame daliban Chadi da ke zanga-zanga
March 11, 2016Wadanda suka shaidar da lamarin sun bayanna cewar 'yan sanda sun tarwatsa daliban ne a lokacin da suke maci a birnin Moundou da ke zama cibiyar 'yan adawan Chadi. Sai dai ministan ilimi mai zurfi na wannan kasa Mackaye Hassane Taisso ya ce daliban sun yi karar tsaye ne ga harkokin ilimi a wasu makarantu na sekandaren birnin.
Watanni shida daliban na Chadi suka shafe ba tare da samun ko da kobo ba daga gwamnati. Amma kuma zanga-zangar ba ta rasa nasaba da tayar da kayar baya da matasa ke yi a kasar da nufin nuna adawa da takarar shugaban kasa Idriss Deby Itno a zaben 10 ga watan Afirilu mai zuwa.
Ita dai gwamnati Chadi ta na fama da karancin kudin shiga tun bayan da farashin danyen mai ya fadi kasa warwas a kasuwannin duniya, Lamarin da ya sa ta gaza ko take lati wajen biyan ma'aikata da dalibai hakkinsu a wasu lokutan.