An kamalla taron Global Media Forum
June 5, 2009Bayan yini ukku na mahaurori, da yammacin yau ne aka zo ƙarshen taron Global Media Forum karo na biyu, wanda Redio DW ta shirya a nan birnin Bonnn.
Jim kaɗan kamin rufe wannan babban taro, saida aka gabatar da ƙarin mahaurori a game da ingancin sabin kafofin sadarawa kamar su Internet, SMS, da makamantansu, da kuma irin yadda ya cencenta ayi amfani da su don cimma manufar zaman lafiya.
A ɗaya wajen, an gabatar da wata mahaura a kan batun dokar tace labarai da gwamnatoci ke ƙargamawa kafofin sadarwa.
Ra´ayoyi sun bambata a dangane da wannan doka.
A lacca da ya gabatar ,Pr Hussain Amin, na jami´ar birnin Alƙahira a ƙasar Masar, yace dokar tace labarai ta zama wajibi ga kafofin sadarwa ta la´akari da yadda wasu labaran duk da cewar gaskiya ne ke zama umal ibasar tada hasumi tsakanin jama´a.
"Ɗari bisa ɗari na amince da tace labarai, kamar yadda na amince da baiwa ɗan jarida cikkaken ´yancin ya faɗi albarkacin bakinsa da zaran dai abinda zai faɗan, ba zai zama aibu ba, ga rayuwar jama´a.
Amma ina jawo hankali masu tunanin cewar a baiwa´yan jarida´yanci ɗari bisa ɗari kuskure ne, wannan batu bai ma taso a cikin aiki jarida , indai ana buƙatar kafofin sadarawa su taka rawar gani wajen shinfiɗa zaman lafiya."
A cikin jawabin rufe taro da ya gabatar,Darakta Janar na DW Erick Bettermann, ya bayyana matuƙar gamsuwa ga sakamakon da aka cimma.
"A tsawan kwanaki ukku na mahaurori na fahinci yadda mahalarta taron suka nuna shawa da buƙatar yin amfani da kafafofin sadarwa domin samar da zaman lafiya a duniya, mahaurorin da aka yi su shaidi cewar ´yan jarida da kafofin sadarwa a shirye suke ,su gama ƙarfi da ƙungiyoyin masu kansu da gwamnatoci a game da manufar samar da zaman lafiya cikin duniya"
Erick Bettermann, ya gayyaci mahalarta taron Global Medias Forum, sunyi amfani da ilimin da suka samu a taron domin, taimakawa a yankuna dabam dabam da suka fito wajen tabatar da zaman lafiya:
"Na yi imanin cewar mahaurorin da muka shirya a babban ɗakin shawara da kuma cikin ƙananan komitoci zasu taka rawar gani wajen cimma burin da muka sa gaba, wato kwanciyar hankali ko ina cikin wannan duniya.kaiwa ga wanda mataki na buƙatar masanyar labarai,husa´o´i da ra´ayoyi tsakanin´yan jarida dake aiki a yankunan dabam dabam-baban yauni ya rataya kanmu na tabbatar da wanan muradi".
Taron Global Media Forum karo na ukku zai gudana daga 21 zuwa 23 gawatan Juni na shekara ta 2010.
A wannan karo mahalarta taron zasu masanyar ra´ayoyi a game da aikin da ya rataya kan kafofin sadarawa wajen yaƙi da ɗumamar yanayi, batun da ya zama ruwan dare gama duniya.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi.
EDita: Hauwa Abubakar Ajeje