An kama masu buga kudin jabu a Spaniya
March 3, 2024Talla
'Yan sanda sun ce miyagun sun samar da kudaden bogin da ya suka kai kimanin euro miliyan daya a takadar kudi ta euro dari-dari. Rundunar 'yan sandan Spaniya ta ce, za a iya rarraba jabun kudaden a injinan ATM ba tare da an sani ba.
Tuni dai jami'an suka ce sun kama mutum 14 daga biranen Barcelona da kuma Rome ciki har da shugaban kungiyar.
Tun a watan Nuwamban bara ce dai 'yan sanda suka baza komarsu bayan da aka gano jabun kudade na yawo a birnin Barcelona.