1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a kama sojoji 200 a Turkiyya

Abdul-raheem Hassan
December 14, 2018

Hukumomin kasar Turkiyya sun kaddamar da sabon samame kan wasu dakarun kasar da ake zargi da hannu a yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Recep Tayyip Erdoğan a shekarar 2016.

https://p.dw.com/p/3A7k6
Türkei Grenze Syrien Idlib Provinz Armee
Hoto: Getty Images/AFP/I. Akengin

Gwamnatin Tukiyya na zargin sojojin da alaka da fitaccen malamin addinin Islama Fethullah Gulen da ake zargi da shugabantar kungiyar ta'addanci tare da yunkurin juyin mulki, sai dai malamin da ke samun mafaka a Amirka ya sha musanta zargin.

Sama da mutane dubu 50 ne aka tsare wasu ma'akata dubu 130 suka rasa aiki tun bayan da aka yi yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Recep Tayyip Erdoğan a shekarar 2016.