1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mali: An kai wa dakarun MINUSMA hari

July 7, 2023

Wasu mutane dauke da makamai sun kai wa ayerin motocin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya Duniya hari a birnin Gao da ke Arewacin Mali.

https://p.dw.com/p/4Tb0h
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Wata majiya daga rundunar MINUSMA ta shaida wa kamfanin dillacin labarun Faransa na AFP cewar 'yan bindigar da ba a kai ga tatancesu ba sun buda wuta a kan ayarin motocin a yayin da suke kan hanyarsu ta ficewa daga kasar. Harin ya haddasa tuntsirewar wata tankar mai inda ta jikkata wani farar hula guda, a sakamakon wucin gadi da rundunar ta fidda.

A ranar 30 ga watan Yuni da ya gabata ne dai kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kwashe dakarun MINUSMA su sama da 12.000 daga Mali bisa bukatar gwamnatin mulkin sojan kasar.

Dama dai 'yan ta'adda masu biyyaya ga Al-Qaida da IS a Mali na yawaita kai hare-hare a barikokin dakarun na MINUSMA dake jibge a kasar tun shekarar 2013.