Harin 'yan bindiga ya halaka mutane da dama
December 26, 2023
Tun dai a daren ranar Asabar da ta gabata ce aka soma fuskantar hare haren yan bindiga a tsakanin yankunan na Filato har zuwa dare jiya Liktin, kuma wani mazaunin yankin gundumar Mbar, da ke karamar Bokkos, Edward Silas wanda tsohon Kansila ne a yankin, ya shaida cewar hare-haren 'yan bindiga sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, kuma wasu daruru sun sami raunuka inda yanzu haka suna kwance a asibitoci suna jiyyar raunuka da suka samu.
Kabin Bayani: An tabbatar wa PDP kujerar gwamna a Filato
Babu bayanai na alkaluma a hukumance kan adadin mutane da suka rasa rayukansu sanadiyar hare-haren 'yan bindiga wanda wasu ke zargi Fulani ne da aikatawa, to amma ta wayar tarho shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar Filato, Nura Abdullahi ya ce Fulani sun yi hasarar rayuka a hare-haren na 'yan bindiga.
Wani Manomi da ke yankin Mr Danjuma Mabas ya shaida cewar mutanenn Barkin Ladi da Mangu ma hare-haren ya shafe su to amma lamarin yafi kamari ne a karamar hukumar Bokkos inda yanzu haka suke kokarin binne mutanen da lamarin ya shafa.
Komandan rundunar da ke wanzar da zaman lafiya a jihar Filato Manjo Janar Abdulsalam Abubakar ya yi alwashin zakulo mutanen da ke da hannu a wannan aika-aikar. A wani jawabi da ya gabatar jim kadan bayan taron majalisar tsaro ta jihar Filato, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar ya bayyana cewar sun gano wasu daga irin kayyayakin da maharan suka yi amfani da su lokacin da suke kai harin. Yanzu haka dai ana zaman zullumi da alhini a yankuna da maharan suka yi wa kawanya a 'yan kwanakin nan.