1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari kusa da masallaci a London

Yusuf Bala Nayaya
June 19, 2017

Wasu rahotanni na zargin cewar wannan hari ne da ke nuna karuwar masu kin jinin addinin Islama a wannan birni na Birtaniya mai al'ummomin kasa da kasa.

https://p.dw.com/p/2euCh
Fahrzeug rast in Gruppe Muslime - mehrere Opfer
Hoto: Reuters/Y. Mok

Mutum guda daya ne ya rasu yayin da wasu takwas suka sami raunika cikin daren jiya bayan da wani da ke cikin mota ya afkawa masu ibada a Arewacin London, lamarin da 'yan sanda suka ce akwai yiwuwar aniya ta ta'addanci a cikinsa.

Cibiyar kula da lamuran addini a Birtaniya ta ce mutumin da ke cikin motar daukar kayan ya afkawa mutane ne da suka fito daga masallaci bayan sallar Tarawi a masallacin Finsbury Park, da ke zama daya daga cikin manyan masallatai a Birtaniya.

'Yan sanda dai sun bayyana cewa da faruwar lamarin suka kai dauki ga mutanen a hanyar nan ta Seven Sisters da ke birnin na London an kuma kama daya cikin maharan da ke zama dan shekaru 48 bayan da sauran biyu suka arce. Theresa May dai ta bayyana cewa wannan hari ne irin na ta'addanci da shi ma magajin birnin London Sadiq Khan ya ce 'yan sanda sun shiga bincike kan harin da ke zama na ta'addanci mai barazana ga 'yanci da zamantakewa.