1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari kan masu yawon bude ido a Masar

Ramatu Garba Baba
July 14, 2017

Wani mutum dauke da wuka ya afka wa baki masu yawon bude ido inda ya yi saurin halaka wasu Jamusawa biyu tare da raunata wasu hudu a wannan Juma'ar.

https://p.dw.com/p/2gaKs
Angriff auf Hotel in Hurghada Ägypten
Hoto: imago

Ma'aikatar tsaron kasar Masar ta tabbatar da harin da ya kashe Jamusawa biyu da kuma raunata wasu hudu a wani wajen shakatawa na Red Sea Resort da ke garin Hurghada. Daga cikin wadanda suka ji raunin dai akwai wata 'yar kasar Rasha sai dai ba a kaiga tantance sauran mutanen da maharin ya raunata ba. Ma'aikatar ta ce dukkanin mutanen da harin ya rutsa da su masu yawon bude ido ne daga kasashen Turai. Ta kuma ce maharin ya yi amfani da wuka lokacin kai harin na wannan Juma'; kuma dukkanin Jamusawan biyu da suka rasa rayukansu, mata ne.

Manjo Janar Mohammed El-Hamzawi, babban jami'in da ke kula da yankin na Hurghada, ya ce maharin ya far ma bakin a ginin Otel din da suka sauka, ya kuma ce an yi nasarar cafke shi, sai dai har yanzu ba a kammala tantance dalilansa na kai harin ba. Kasar Masar dai ta ayyana dokar ta baci sanadiyar mummunan harin da aka kai kan majami'u biyu a farkon wannan shekara da ya yi sanadiyar rayukan mutane fiye da 40, yayin da a daya hannun bayanai ke cewa ana ci gaba da yakar mayakan kungiyar IS da suka addabi kasar da hare-haren ta'addanci.