An kai hare-hare a cocinan Kaduna
June 17, 2012Talla
Mutane fiye da 20 suka rasa rayuka, sannan kimanin wasu 100 su ka ji raunuka, a cikin wasu tagwayen hare-haren ƙunar baƙin wake a cocinan biranen Kaduna da Zariya dake arewacin tarayya Najeriya.
Har yanzu dai babu ƙungiyar da ta ɗauki alhakin kai wannan hari, amma makon da ya gabata,ƙungiyar Boko Haram ta yi shelar ɗaukar alhakin kai hare-hare masu kama da wannan a daidai lokacin da mabiya addinan kirista ke aiyukan ibada.
Jim kaɗan bayan kai hare-haren, matasan kirsitoci sun fito a tinuna domin nuna ɓacin rai.
A wani mataki na riga kafin bazuwar tashe-tashen hankula, gwamnatin jihar Kaduna ta kafa dokar ta ɓacin sa' o' i 24.
Mawallafi:Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu