Muhammadu Buhari ya yi rantsuwar kama aiki a Najeriya.
Ubale Musa May 29, 2015
Sabon shugaban kasa a Tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi mulki a wannan Jumma'a 29 ga watan Mayu na 2015, a dai-dai lokacin da kasar ke fuskantar kalubalen rashin tsaro da matsanancin yanayin tattalin arziki.