An kafa gwamnati a Sudan ta Kudu
February 22, 2020Talla
Hakan na zuwa ne bayan yarjejeniyar da shugaban kasar Salva Kiir da madugun adawar suka cimma kan kafa gwamnatin hadaka domin kawo karshen rikicin da aka kwashe shekaru shida ana yi, wanda kuma ya lakume rayukan al'umma.
Bayan da ya sha rantsuwar kama aiki, Riek Machar ya yi wa al'ummar kasar albishir da cewar zai yi aiki da shugaban kasar domin kawo karshen wahalhalun da suke ciki.
Shugaba Salva Kiir ya jinjina wa wannan matsaya da aka cimma tare da cewar karshen yaki ya zo a Sudan ta Kudu.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Riek Machar da Shugaba Kiir ke kokarin shugabantar jaririyar kasar ba, amma bambance-bambance ke hana su tafiya tare.