1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An jinkirta zaben 'yan majalisar Chadi

February 3, 2017

Shugaba Idris Deby na Chadi ya jinkirta zaben 'yan majalisar dokokin kasar saboda matsalolin rashin kudi da kasar ta samu kanta a ciki.

https://p.dw.com/p/2Wx7q
Tschad Präsident Idriss Deby
Hoto: Getty Images/F.Belaid

Shugaba Idriss Deby na kasar Chadi ya bayyana sake dage zaben 'yan majalisar dokoki da tun farko aka tsara a shekara ta 2015, saboda rashin kudade da ake fuskanta a kasar mai arzikin man fetur, wadda ta shiga mawuyacin hali sakamakon faduwar farashin mai a kasuwar duniya.

Shugaba Deby ya bayyana jinkirta zaben lokacin da yake ganawa da 'yan jarida, bayan komawa gida daga taron shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Afirka da ya gudana a birnin Addis Ababa na kasar Habasha. Sannan Deby ya nemi 'yan adawa su shiga tattaunawa da gwamnatinsa. Shi dai Shugaba Idriss Deby yana rike da madafun ikon kasar ta Chadi tun shekara ta 1990, kuma ya tabbatar da cewar da zaran kasar ta samu kudaden da take bukata za a shirya zaben 'yan majalisar dokokin.