Haramta wa tshohon shugaban Brazil takara
September 1, 2018Talla
Wannan dai ya sanya kasar ta Brazil da ke zama babba a yankin Latin Amirka ta shiga rashin tabbas kan wanda ke zama fitaccen dan takarar shugabancinta a zaben watan Oktoba.
A zaman da alkalan kotun suka yi dai, shida ne cikin alkalan kotu bakwai ba su goyi bayan takarar ta Lula da Silva ba saboda tuhumar da ake masa da ta shafi cin hanci da rashawa har ta kai ga tsare shi kan tuhumar da tsohon shugaban ya ce ba ta da tushe.
Jam'iyyarsa ta Workers' Party ta sha alwashi na daukaka kara kan sakamakon hukuncin alkalan kotun zaben a Brazil, sai dai da dama na ganin daukaka karar ba lallai ta yi tasiri ba saboda shari'ar da ke gaban tsohon shugaban kafin zaben na Oktoba.