Akwai Turkawa masu yawa a Jamus da Sweden
June 21, 2018Talla
Ana saran Tayyip Erdogan zai sake lashe zaben Lahadin, bayan nan a bawa shugaban kasar sabbin madafan iko. Tuni dai rigingimu suka mamaye yakin neman zabe, a yayin da 'yan adawa suka koka da rashin basu damar amfani da kafofin yada labarun kasar.
Haramtawa 'yan majalisar Jamus da Sweden da ke zama kasashe biyu da ke da mafi yawan al'ummar Turkawa a Turai, zai kara assasa damuwa a zukatan kungiyoyin kare hakkin jama'a dangane da yiwuwar yin magudi, saboda babu masu sa ido.