An hallaka jakadan Rasha da ke Turkiyya
December 19, 2016Talla
Kamfanin dillancin labarai na RIA mallakin gwamnatin Rasha ya ce jakadan mai suna Andrey Karlov ya rasa ran nasa bayan raunuka da ya samu sakamakon wannan harbi kuma tuni fadar mulkin Rasha ta Kremlin ta danganta harin a matsayin aiki na ta'addanci. Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashe ciki kuwa har da Amirka sun yi Allah wadai da kisan Mr. Karlov inda suka bukaci lallai a gudanar da bincike don bakado wanda ke da hannu a kisan. A share guda magajin garin Ankara Melih Gökçek ya ce tuni suka kara matakan tsaro a ofishin jakadancin Turkiyya da ke birnin kana ya ce kisan Mr. Karlov wani yunkuri na dagula dangantaka tsakanin Rasha da Turkiyya.