1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar hare-hare a Afirka ta Tsakiya

Ramatu Garba Baba
June 23, 2020

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya gargadi kungiyoyi na masu gwagwarmaya da makamai a Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya da su mutunta yarjejeniyar zaman lafiya su daina kai hare-hare kan jama'a.

https://p.dw.com/p/3eBGu
Zentralafrikanische Republik | Naturschutz in Krisengebieten | Soldaten vor dem Präsidentenpalast in Bangui
Hoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya gargadi kungiyoyi masu gwagwarmaya da makamai a Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya da su mutunta dokar tsagaita bude wuta ko kuma ta dauki matakin ladabtarwa a kansu. Gargadin yiyuwar sanya musu takunkumin, ya biyo bayan watsi da kungiyoyin suka yi da yarjejeniyar da aka kulla a bara, inda suke ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula da rundunar da majalisar ta tsugunar don kiyaye zaman lafiya. Na baya-bayan na shi ne harin da ya yi sanadiyar rayukan sojoji biyu da raunata wasu bakwai a ranar Lahadin da ta gabata.

Shugaban rundunar tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, Jean-Pierre Lacroix a yayin da ya ke jawabi a gaban kwamitin, ya ce jama'a da sauran kungiyoyi da ke aikin jin kai na rayuwa cikin yanayi na fargaba saboda barazanar da suke fuskanta daga kungiyoyi, abin da ya ce sam, ba za a lamunta ba.

Tun daga shekarar 2013 Afrika ta Tsakiya ta fada cikin rikicin kabilanci da addini a tsakanin 'yan tawayen Seleka Musulmi da kungiyar Kristoci 'yan banga ta anti-Balaka, dubban rayuka sun salwanta kafin a cimma sulhu, ana ganin sabbin hare-haren basa rasa nasaba da babban zaben kasar da aka shirya gudanar a watan Disambar wannan shekarar ta 2020.