An gano sansanin hada nukiliyar sirri a Koriya ta Arewa
November 12, 2018Talla
A watan Yuni ne dai Shugaba Trump ya yaba da ganawarsa da Shugaba Kim Jong Un matakin da ya bude kofar watsi da shirin hada makaman na nukiliya bayan da Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu suka hayayyako wa juna tamkar an fada yanayi na yaki.
Tun dai ganawar da aka yi a Singapore, Koriya ta Arewa ta tsayar da gwajin makamin nukiliya da makami mai linzami, dama rushe wurin da take gwajin na makamin nukiliyar da yin alkawari na rusa babbar tashar hada nukiliyar. Sai dai masu bincike daga cibiyar tsare-tsare da nazarin harkokin kasa da kasa a birnin Washington na Amirka sun bayyana cewa sun gano sansanoni 13 wadanda gwamnatin Koriya ta Arewa ba ta bayyana su ba, koma za su iya kaiwa 20.