1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano bakin zaren warware rikicin ƙasar Yemen

November 24, 2011

Yemen ta kama hanyar kawo ƙarshen boren neman kawo ƙashen mulkin shugaban ƙasar bayan da ya sanar da miƙa mulki ga mataimakin sa

https://p.dw.com/p/13GGk
Boren neman kawar da shugaba Saleh daga mulki a birnin SanaaHoto: picture alliance / dpa

Shugaba Ali Abdallah Saleh na ƙasar Yemen ya miƙawa mataimakin sa ragamar jagorancin ƙasar a wannan Larabar. Tuni kuma al'ummomin ƙasa da ƙasa suka yi marhabin lale da matakin daya ɗauka, amma 'yan adawar ƙasar sun buƙaci gurfanar da shi a gaban shari'a kana al'ummar ƙasar ta ci gaba da gudanar da ƙarin zanga-zanga. A ƙarƙashin wata yarjejeniyar da shugaba Saleh ya sanyawa hannu dai, cikin tsukin kwanaki 30 dake tafe ne zai miƙa ɗaukacin harkokin mulki ga mataimakin na sa Abd-Rabbo Mansour Hadi. Bayan haka ne kuma za'a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa cikin kwanaki 90. Kazalika yarjejeniyar ta baiwa shugaba Saleh da iyalansa dama muƙarraban sa tabbacin samun kariya daga gurfana a gaban ƙuliya bayan miƙa mulkin. A martanin da ta mayar, kantomar kula da manufofin ƙetare na ƙungiyar tarayyar Turai Catherin Ashton ta kwatanta yarjejeniyar da cewar buɗe wata muhimmiyar ƙofa ce, kana ta buƙaci Yemenawa da su mutunta yarjejeniyar da zuciya ɗaya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu