1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara samun rikici gabannin zaben Gini

Abdoulaye Mamane Amadou AS
October 8, 2020

An soma samun tashin hankali gabannin zaben shugabancin kasar Gini na ranar 18 ga wannan watan. Rikici dai na cigaba da wakana tsakanin 'yan adawa masu fafatukar taka burki ga shugaba Alpha Conde da ke son tazarce.

https://p.dw.com/p/3jckJ
Guinea Wahlen in Conakry
Hoto: Getty Images/AFP/C. Binani
Guinea Protest in Conakry
Gabannin zaben Gini, 'yan kasar sun yi bore kan shirin tazarce Shugaba KondeHoto: AFP/C. Binani

Bangarorin siyasar Gini dai sun barke da kalamun batanci da kabilanci, kama daga dandalin tarukansu na siyasa har zuwa ga dandalin sada zumunta na zamani a daidai lokacin da ake dab da gudanar da zaben na ranar 18 ga wannan watan. Wannan lamarin da 'yan siyasar kasar suka runguma ya janyo ramuwar gayya a fannoni dabam-dabam, wadanda suka hada da yayyaga tutocin babbar jam'iyyar adawa ta UFDG a gabashin kasa da kai farmaki ga firaminsitan kasar a lokacin da yake tsaka da gangamin yakin neman zabe a yankin nan na Labe.

Tuni dai wannan lamarin ya fara tayar da hankulan masu hankoron shimfida zaman lafiya ciki har da kungiyoyyin fararen hula da malaman addinai irinsu El hadj Djeriba Diabi, wanda yake cewar "muna tsananin bukatar samun zaman lafiya da yin rayuwa mai tsafta a lokutta da kuma bayan zabe, kana muna bukatar cikakken zabe na gaskiya a cikin adalci ba tare da wata amaja ba." 

Kiraye-kirayen jama'ar dai baya rasa nasaba ne da irin tashe-tashen hankulan da aka lura an samu a kasar da kuma suka yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane, kuma kamar kowa ne lokaci a nasu bangare kungiyoyin fararen hula sun ambaci tura jami'an sa ido a manyan zabukan da ke tafe duk da fargabar da ake da ita taa yiwuwar tashe-tashen hankula. 

Tuni Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar ECOWAS suka aika tawaga ta musamman kasar ta Guinea don ganawa da bangarorin da ba sa jituwa a wani yunkuri na samun zaben a cikin natsuwa, kan daga bisani tawagar ta wuce zuwa kasar Cote d'ivoire wacce ita ma ke shirin shiga zabe a cikin yanayi na fargabar tashe-tashen hankula.