1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An daure dan jarida shekaru uku a Turkiyya

Abdul-raheem Hassan
November 21, 2017

Wata babbar kotu a birnin Instanbul, ta yanke wa editan yanar gizo na babban jam'iyar adawar kasar hukuncin daurin shekaru uku da wata guda a gidan yari bisa laifukan ta'addanci.

https://p.dw.com/p/2nzsh
Türkei Istanbul Proteste gegen Anklagen von Cumhuriyet-Journalisten
Hoto: Imago/Depo Photos

Kotun ta kama dan jarida Oguz Guven da laifuka biyu, da suka hada da yada farfagandan 'yan ta'addan kasashen ketere kuma yin alaka da kungiyar Fetula Gulen malamin da gwamnatin Turkiyya ta zarga da yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Racceb Tayyib Erdogan a shekarar 2016, zargin da malamin ya musanta.

Wannan dai ba shi ne karon farko da gwamnatin Turkiyya ke fakon gidan jaridar Daily mai yada labarabarai a yanar gizo ba,  abin da 'yan kasar ke kalubalantar gwamnati na neman sawa 'yancin fadin albarkacin baki takunkumi.

A yanzu dai akwai 'yan jaridu 170 na tsare a gidajen yarin kasar Turkiyya, wannan ya sa wani rahoton baya-bayannan kan 'yancin 'yan jaridu a duniya ya nuna Turkiyya a mataki na 155 a jerin kasashen duniya 180.