1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An dakatar da shugabar Brazil daga kan mulki

Gazali Abdou TasawaMay 12, 2016

Da kuri'u 55 ne daga daga cikin 81 majalissar dattawan kasar ta brazil ta amince da matakin tsige shugabar wacce ake zargi da aikata almundahana.

https://p.dw.com/p/1ImE6
Brasilien Dilma Rousseff
Hoto: Reuters/U. Marcelino

An dakatar da Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff daga kan kujerarta ta mulki bayan da majalisar dattawan kasar ta kada kuri'ar amincewa da tsigeta daga kan mukamin nata.

Da kuri'u 55 ne daga daga cikin 81 majalissar dattawan kasar ta brazil ta amince da matakin tsige shugabar wacce ake zargi da aikata almundahana.

A nan gaba kadai a wannan rana ta Alhamis ne, za a maye gurbinta da mataimakinta Michel Temer. Wannan mataki na majalisar dattawan kasar ta Brazil shi ne tsani na karshe na kai wa ga gurfanar da ita a gaban kuliya domin ta kare kanta daga zargin cin hancin da ake yi mata.

Ana sa ran dai zaman shari'ar zai kawo karshe nan da watannin shida masu zuwa.